Ba zai yiwu ku fadi wani mummunan abu game da Buhari ko ku zage shi ba – Sanata Gaya ga yan Najeriya

Ba zai yiwu ku fadi wani mummunan abu game da Buhari ko ku zage shi ba – Sanata Gaya ga yan Najeriya

Sanata Kabiru Gaya (APC-Kano ta Kudu) ya bukaci mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo da ya yi watsi da zargin dan majalisa na biyu, Junaid Mohammed akansa da ke cewa yana nuna son kai.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa Gaya, wanda yayi magana ga manema a fadar Shugaban kasa a ranar Talata, 22 ga watan Oktoba, bayan wata ganawar sirri da Osinbajo a Villa, Abuja, ya bukaci Mohammed da ya duba bayani kafin ya yi magana.

An rahoto cewa a kwanan nan ne Mohammed ya yi zargin cewa mafi akasarin mutanen da Osinbajo ya ba mukami sun fito ne daga kabilarsa da kuma mambobin cocinsa.

Gaya ya bayyana cewa Shugaban kasa da mataimakin Shugaban kasa sun cancanci mutuntawa daga dukkanin yan Najeriya.

"Da farko dai, wannan na da kyau; kun gani a kasa irin Najeriya, muna bukatar mutunta dattawanmu; mutane kama shugaban kasa Muhammadu Buhari, ba zai yiwu ku fadi wani mummunan abu game dashi ko ku zage shi ba saboda shi shugaban kasa ne."

"Haka zalika, matamakin shugaban kasar, babu wani amfani tayar da dukkanin wadannan zantuka; ina ganin akwai bukatar kafin Junaid ya yi magana, ya kamata ya duba tarihi na wadanda ke aiki a ofishin mataimakin shugaban kasa."

Akan zaben gwamnan mai zuwa a jihar Kogi, Gaya ya bayyana cewa a matsayinsa na Shugaban, kwamitin majalisar dattawa kan hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), kwamitin ta samu jawabi daga INEC kan shiinta na zaben.

KU KARANTA KUMA: Mata 9, maza 7 sun samu shiga jerin kwamishinonin Gwamna Abdulrazaq

A cewarsa, mambobin kwamitin za su kai ziyarar gani da ido jihar sannan su ga yadda suka shirya ma zaben.

Gaya ya kara da cewa kwamitin zai taimakawa INEC don tabbatar da zabe na gaskiya da lumana a Kogi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel