Hukumar kula da alhazan Najeriya ta tare a sabon babban ofishinta a Abuja

Hukumar kula da alhazan Najeriya ta tare a sabon babban ofishinta a Abuja

Hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya ta Najeriya, NAHCON, ta tattara inata inata ta koma sabon ofishinta dake babban birnin tarayya Abuja, a wani gini da ake kira da suna Metro Plaza, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a makonni 2 da suka gabata hukumar ta fara kwashe kayanta zuwa sabon sakatariyar inda sai a ranar Talata, 22 ga watan Oktoba suka kammala tarewar.

KU KARANTA: Dubu ta cika: Sojoji sun yi ram da wani mai cinikin makamai a Kaduna, sun kama AK 47 guda 6

Hukumar kula da alhazan Najeriya ta tare a sabon babban ofishinta a Abuja
Hukumar kula da alhazan Najeriya ta tare a sabon babban ofishinta a Abuja
Asali: Twitter

Tun a shekarar 2017 hukumar ta sayi sabuwar sakatariyar, kamar yadda shugaban sashin hulda da jama’a na hukumar, Fatima Usara ta tabbatar, inda tace an sayi sakatariyar a kan kudi naira biliyan 2.4.

Usara ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta baiwa hukumar kudi naira miliyan 587, yayin da hukumar Hajjin ta tara sauran cikon kudin ta hanyar kudaden dake tarawa da kuma kudaden dake tatsa a matsayin kudaden shiga.

Domin kaddamar da ofishin, shuwagabannin hukumar sun gudanar da taro a sabuwar sakatariyar a karkashin jagorancin mukaddashin shugaban hukumar, Abdullahi Muhammad, kwamishinan ayyuka Alhaji Abdullahi Saleh da sauransu.

A wani labarin kuma, An karrama wata mata a jahar Kaduna, Amina Abubakar, wanda ta ciri tuta a tsakanin iyaye mata a jahar ta bangaren kwarewa wajen iya da shayar da jariransu na tsawon lokaci.

Sanin kowa ne shayar da nonon uwa ga jarirai abu ne mai matukar muhimmanci ga lafiyar jarirai kamar yadda addinin musulunci ya yi nuni, haka suma masana ilimin kiwon lafiya suna baiwa mata kwarin gwiwar aiwatar da wannan tsari domin a samu al’umma mai koshin lafiya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel