Yadda N100 ya sanya direban mota kashe dan kungiyar sufuri

Yadda N100 ya sanya direban mota kashe dan kungiyar sufuri

Wata kotun Majistare ta Ado Ekti ta yi umurnin tsare wani direban motar haya mai shekara 20, Ismaila Bello kan zargin kisan kai.

Bello na fuskantar shari’a akan zargin kashe wani mamba na kungiyar suuri, Femi Ajayi, a Igogo Ekiti, karamar hukumar Moba da ke jihar Ekiti.

Dan sanda mai kara, Inspekto Oriyomi Akinwale, ya fada ma kotu cewa wanda ake karan ya aikata laifin ne a ranar 25 ga watan Satumba, 2019, kan harajin N100 da suke biya kullun.

Akinlade yace, “kungiyar ta ba wanda ake karan, wanda ya kasance direba, tikitin N100 na kullun. A hanyarsa ta dawowa, sai aka nemi ya biya kudin tikitin amma sai ya ki.

“A cikin haka, sai ya zama rigima sannan daya daga cikin mambobin kungiyar ya sace masa tayar mota, wanda hakan ya tunzura shi sannan yayiwa marigayin duka da mummunan asiri. Marigayin ya mutu ne a lokacin da ake hanyar kai shi asibiti."

A cewarsa, laifin ya kara da sashi na 319(1) na dokar jihar Ekiti, 2012.

KU KARANTA KUMA: Mata 9, maza 7 sun samu shiga jerin kwamishinonin Gwamna Abdulrazaq

Dan sandan ya bukaci kotu da ta tsare wanda ake karan a gidan gyara halayya zuwa lokacin da za a ji shawarar da za a yanke.

Ba a saurari rokon wanda ake kara ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel