Yanzu-yanzu: An sake bankado gidan gyara kangararru a Adamawa

Yanzu-yanzu: An sake bankado gidan gyara kangararru a Adamawa

Jami'an yan sandan Najeriya sun ceto mutane 15 a wani gidan ladabtar da kangararru mara rijista a jihar Adamawa.

Hukumar yan sandan jihar sun dira gidan ne dake Wuri-Hausa cikin Yola, birnin jihar.

A cewan wani mai idon shaida, yan sanda sun samu matasa 15 da wani tsoho ya tsare da yaran aikinsa masu kula masa da gidan.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Suleiman Yahaya Ngoroje, ya tabbatar da labarin inda ya ce jami'an hukumar sun kai simame gidan da yammacin Talata.

Ya ce zai bada karin bayani kai bayan gudanar da bincike cikin lamarin yau.

Yanzu-yanzu: An sake bankado gidan gyara gangararru a Adamawa
Yanzu-yanzu: An sake bankado gidan gyara gangararru a Adamawa
Asali: Facebook

KARANTA Yanzu-yanzu: An yi garkuwa da Alkalin babban kotun tarayya, Justice Abdul Dogo :

A wani labarin mai kama da haka, Bayan biyun da aka bankado a unguwar Rigasan jihar Kaduna, gwamnatin jihar Kaduna ta sake bankado gidajen ladabtar da kangararru biyu marasa rijista a jihar.

Wannan karon, a garin Zariya aka gano gidajen biyu.

Tuni an garzaya da wadanda aka samu cikin gidajen cikin mari zuwa gidan gwamnatin jihar.

Mataimakiyar gwamnan jihar, Hadiza Balarabe, ce ta karbi bakuncinsu tare da sauran manyan jami'an gwamnatin jihar Kaduna.

Hajiya Hadiza ta bayyana cewa za'a kai su asibiti domin dubasu kafin sanin matakin da za'a dauka na gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel