Yanzu-yanzu: An yi garkuwa da Alkalin babban kotun tarayya, Justice Abdul Dogo

Yanzu-yanzu: An yi garkuwa da Alkalin babban kotun tarayya, Justice Abdul Dogo

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da Alkalin babban kotun tarayya dake Akure, birnin jihar Ondo, Justice Abdul Dogo.

An sace Alkali Abdul Dogo a ranar Talata yayinda yake hanyar komawa garin Akure daga birnin tarayya Abuja. The Nation ta bada rahoto.

An samu rahoton cewa masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan Alkalin kuma sun bukaci N50 million kudin fansa.

Hakazalika rahoto ya nuna cewa sifeto janar na hukumar yan sanda ya tura kwamandan rundunar IRT, DCP Abba Kyari, zuwa Akure domin cetosa.

Garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a Najeriya duk da matakan da gwamnati take ikirarin cewa tana dauka.

KU KARANTA: An sake bankado gidan gyara gangararru a Adamawa

A bangare guda, Sojoji sun kama wani gawurtaccen dilalin bindigu da ke sayar wa masu garkuwa da mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja bindigu da sauran makamai.

Dakarun sojojin 1 Division na hedkwatan sojoji a Kaduna ne suka kama Alhaji Shehu a gidansa da ke Sabogaya a karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sojojin sun kuma kama wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a lokacin da suke tattaunawa kan bayar da hayar AK47 da za su yi amfani da shi wurin garkuwa da mutane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel