Mata 9, maza 7 sun samu shiga jerin kwamishinonin Gwamna Abdulrazaq

Mata 9, maza 7 sun samu shiga jerin kwamishinonin Gwamna Abdulrazaq

- Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya aika wasu jerin sunayen zababbun kwamshinoni shida zuwa ga majalisar dokokin jihar

- Hakan ciko ne ga jerin zababbun mutane 16 da ya fara turawa yan majalisar domin tantancewa

- A bisa ga jerin sunayen karshe da kakakin majalisar, Yakubu Danladi ya karanto a zauren majalisar dokokin, mata tara da maza bakwai ne suka samu shiga majalisar

Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, a ranar Talata, 22 ga watan Oktoba, ya aika wasu jerin zababbun kwamshinoni shida zuwa ga majalisar dokokin jihar domin cike jerin zababbun mutane 16 da ya turawa yan majalisar domin tantancewa.

A bisa ga jerin sunayen karshe da kakakin majalisar, Yakubu Danladi ya karanto a zauren majalisar dokokin, a lokacin zaman majalisar a ranar Talata, mata tara da maza bakwai ne suka samu shiga majalisar.

Matan da suka samu shiga jerin sune Hajia Saadatu Modibbo-Kawu, Miss Joana Kolo, Hajia Arinola Lawal, Hajia Aishat Ahman-Patigi, Mrs Afolabi Adenike, Ahmad Fatima, Aremu Deborah, Oyedun Juliana da kuma Oyeyemi Florence.

KU KARANTA KUMA: Babbar magana: Yaki ne yake neman barkewa a jihar Kogi ba zaben gwamna ba - Matar dan takarar gwamnan jihar

Mazan kuma sune Rotimi Iliyasu, Salman Jawondo, Aliyu Kora-Sabi, Dr Raji Razaq, Aliyu Saifudeen, Wahab Agbaje and Murtala Olarewaju.

A halin da ake ciki, kakaki majalisar ya fada ma zababbun kwamishinonin da su gabatar da kwafin takardunsu yayinda za a fara tantance su a ranar Talata.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel