Jami'an tsaro sun kama wata mota dauke da gawawwaki 39 a kasar Ingila

Jami'an tsaro sun kama wata mota dauke da gawawwaki 39 a kasar Ingila

- 'Yan sanda a kudu maso gabas din kasar Ingila sun cafke wata motar daukar kaya dauke da gawawwakin 39

- Direban motar mai shekaru 25 a duniya an gano dan kasar Ireland ne

- Tuni dai jami'an tsaro sun fara bincike tare da kokarin gano ko su waye mamatan

‘Yan sanda a kudu maso gabas din Ingila, sun cafke wata motar daukar kaya da gawawwaki 39 wadanda ake zargin an taho dasu daga Bulgaria.

Babban sufirtandan ‘yan sanda, Andrew Mariner ya ce, a ranar Laraba ne hukumomin ke kokarin gano ko su waye mamatan.

KU KARANTA: Innalillahi: Masu fizgen waya sun hallaka matashi har lahira

‘Yan sandan sun ce, an kirasu ne da gaggawa wajen karfe 1:40 na dare bayan an gano motar daukar kayan kunshe da gawawwakin mutane a Waterglade Industrial Park.

Mariner yace, motar ta shiga kasar ne ranar 19 ga watan Oktoba kuma ‘yan sandan na aiki da sauran jami’an tsaro don bincike.

Direban motar mai shekaru 25 a duniya dan asalin arewacin Ireland ne. Tuni dai ‘yan sanda suka cafkesa da zargin kisan kai.

“Wannan abin alhini ne a ce mutane da yawa haka sun rasa rayukansu,” in ji ‘yan sandan bayan an gano cewa mutanen duk matattu ne.

Tuni aka zuba ‘yan sanda don hana shige da fice a Waterglade Industrial Park din.

“Yan sandan masu hana shige da ficen zasu dau lokaci suna gadin wajen. ‘Yan sandan na cewa za a dau lokaci mai tsawo kafin a gano mamatan.” cewar Brennan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel