Legas: Jigo a jam'iyyar PDP da magoya bayansa sun dunguma sun koma APC

Legas: Jigo a jam'iyyar PDP da magoya bayansa sun dunguma sun koma APC

Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), na jihar Legas, Alhaji Tunde Balogun, ya tarbi jigo a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Tajudeen Agoro da magoya bayansa masu yawa zuwa jam'iyyar ta APC.

The Nation ta ruwaito cewa ya ce ficewar Agoro da magoya bayansa daga jam'iyyar PDP a jihar alama ce da mutuwar jam'iyyar.

Agoro tsohon dan majalisar jihar Legas ne daga 1999 zuwa 2003 kuma shine jami'in kidayar kuri'u na tsohon dan takarar gwamnan PDP a jihar, Mista Jimi Agbaje a 2015 da 2019.

Balogun ya yi murnar tarbar tsohon dan majalisar da ya ce dan uwansa ne, aboki kuma dan siyasa da ke kusanci da talakawa kuma shigowarsa jam'iyyar alheri ne ga APC.

DUBA WANNAN: Kano: An kama buhunnan shinkafa 250 da aka boye cikin tankan man fetur (Hoto)

Balogun ya kara da cewa za a shirya bikin tarbar jigon na PDP da kuma mawaki, Abbas Akande Obesere, Sanata Adeseye Ogunlewe da Cif Remi Adikwu a wata mai zuwa.

Shugaban na yAPC ya ce jam'iyyar tunda fari alheri ne ga al'ummar Legas da Najeriya kuma dama Allah ya kadara za su mulki jihar Legas.

Acewarsa, ana iya ganin alamar hakan duba da yadda jiga-jigan jam'iyyar PDP ke ficewa suna shigowa jam'iyyar APC ciki har da tsohon ministan ayyuka, Sanata Ogunlewe, tsohon shugaban PDP na jihar, Hon. Moshood Salvador da Cif Olawale Cole.

Ya bawa sabbin 'yan jam'iyyar tabbacin cewa za a tarbe su da hannu biyu-biyu kuma za a basu dukkan damar da sauran 'yan jam'iyyar ke da shi domin kowa daya ne a jam'iyyar.

A bangarensa, tsohon dan majalisar ya yabawa namijin kokarin da tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu wanda ya kira jagora mai hangen nesa da zurfin tunani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel