Yanzu-yanzu: Sojoji sun kama wani gawurtaccen dillalin bindigu a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Yanzu-yanzu: Sojoji sun kama wani gawurtaccen dillalin bindigu a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Sojoji sun kama wani gawurtaccen dilalin bindigu da ke sayar wa masu garkuwa da mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja bindigu da sauran makamai.

Dakarun sojojin 1 Division na hedkwatan sojoji a Kaduna ne suka kama Alhaji Shehu a gidansa da ke Sabogaya a karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sojojin sun kuma kama wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a lokacin da suke tattaunawa kan bayar da hayar AK47 da za su yi amfani da shi wurin garkuwa da mutane.

DUBA WANNAN: Jihar Yobe za ta fara amfani da harshen Hausa wurin koyarwa a makarantun frimare

Mataimakin Direktan sashin hulda da al'umma na 1 Division, Kwanel Idimah ya tabbatar da kamen cikin wata sanarwa da ya fitar a Kaduna.

Ya ce an kama dilalin bindigun a ranar Asabar dauke da AK47 guda 6 yayin da sauran mutane biyun da ake zargi kuma an kama su ne lokacin da suke kokarin karbar hayan bindiga daga hannun wani 'dan banga.

Ya ce, "Bayan samun bayanan sirri, sojoji sun bi sahun wani da ake zargi Alhaji Shehu zuwa gidansa a Sabogaya a karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna suka gudanar da bincike suka gano AK47 guda shida.

"Bayan hakan, Shehu ya yi ikirarin cewa daya daga cikin bindigun ne kawai nasa inda ya ce sauran na dansa ne da dan uwansa da surukansa kuma yanzu an fara bincike don kamo sauran wadanda ake zargin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel