Yadda wani uba ya yiwa dansa dukan kawo wuka har lahira a jihar Neja

Yadda wani uba ya yiwa dansa dukan kawo wuka har lahira a jihar Neja

Rundunar yan sanda ta kama wan mutum ma suna brahm Mohammed, mazaunn Makunkele da ke karamar hukumar Bosso a jhar Neja, kan zargn dukan dansa ma shekara tara har lahira.

Jami’an yan sandan yankn Paiko ne suka kama ma lafin biyo bayan rahoton da suka samu daga wan Abubakar Adamu na kauyen Yidna dake Paiko.

Jaridar Punch ta ruwato cewa anyi wa marigayin wanda ke taya mahafinsa kiwo duka har lahira saboda wani laifi da ya yi.

An tattaro cewa mai laifin ya yiwa dan nasa duka da bulala har sai da ya mutu sakamakon cigaba da dukan nasa.

A wata hira da manema labarai, Mohammed wanda ya yi danasani akan lamarin, yace bai da kudrn kashe dansa, inda ya kara da cewa kawai yana kokarin ladabtar dash ne lokacin da lamarin ya afku.

KU KARANTA KUMA: Mutane da dama sun jikkata, an fasa shaguna yayinda yan sandan SARS da mazauna wani yanki suka kara a jihar Taraba

“Dana bai kasance mai gaskiya ba akan lamura: Raina y abaci dashi sannan zuciyana ya dauk zafi lokacin da nake dukan sa. Abun bakin ciki, ya mutu. Ina matukar nadama akan abunda na aikata,” inji shi.

Kakakin yan sandan jihar, Muhammad Abubakar wanda ya tabbatar da lamarin yace an rigada an sanya tuhuma kan mai laifin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel