Wallahi na dauka budurwa ce, ban san cewa gardi ne irina ba - In ji mutumin da ya zabgawa shahararren Dan Daudun nan na Legas mari

Wallahi na dauka budurwa ce, ban san cewa gardi ne irina ba - In ji mutumin da ya zabgawa shahararren Dan Daudun nan na Legas mari

- Mutumin da ya zabge Bobrisky da mari a jihar Legas ya bayyanawa manema labarai yadda lamarin ya faru

- Mutumin ya bayyana cewa shi ya zaci cewa Bobrisky budurwa ce tun farko shine yasa bai dauki wani mataki ba

- Ya ce sanadiyyar buga masa motar da Bobrisky yayi ya sanya bayan motar shi ya lalace baki daya

Mutumin da ya zabgawa shahararren dan Daudun nan na jihar Legas Bobrisky mari, bayan ya buga masa bayan mota, ya bayyana yadda lamarin ya faru, bayan an kamo shi.

Da yake magana da manema labarai a wani shagon sayar da waya, mutumin ya dora laifin wannan abu akan Bobrisky da ya kasa taka birkin motarsa. Haka kuma ya bayyana cewa a dalilin wannan lamari bayan motar shi ya lalace baki daya, amma kuma babu abinda ya samu motar Bobrisky.

KU KARANTA: Kishi kumallon mata: Budurwa ta kashe kanta bayan ta samu fina-finan batsa a wayar saurayinta

Haka kuma ya bayyana cewa ya bawa dan Daudun hakuri a lokacin da lamarin ya faru, amma kuma yaki yadda ya janye motar shi. Bayan haka kuma ya bayyana cewa ya dauka Bobrisky budurwa ce, shine ma ya saka bai dauki mataki ba tun a lokacin, amma dole ya saka ya harzuka bayan Bobrisky ya dauke mishi waya.

Mutumin ya bayyanawa manema labarai cewa 'yan sanda sun nemi ya siyawa Bobrisky sabuwar waya bayan sabuwar wayar da aka siya masa iPhone 11 max ta samu matsala sanadiyyar wannan lamari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel