Bidiyo: An kama wani mai sayar da karas yana wanke karas din da zai sayarwa mutane da ruwan kwata mai datti

Bidiyo: An kama wani mai sayar da karas yana wanke karas din da zai sayarwa mutane da ruwan kwata mai datti

- Asirin wani mutumi ya tonu bayan an kama shi dumu-dumu yana wanke karas din da zai sayarwa da mutane da ruwan kwata

- Yayin da aka nuno mutumin yana wanke karas din a cikin kwatar a gefe daya kuma an nuno wani can yana yin fitsari a kwatar

- Wannan rahoto dai tamkar gargadi ne ga mutane masu sayen kaya irin wannan su ci ba tare da wankewa yanda ya kamata ba

Asirin wani mutumi mai sayar da karas ya tonu bayan an kama shi da ranar Allah yana wanke karas da cucumber da zai sayarwa mutane da ruwan kwata mai datti.

Wannan abu da mai sayar da karas din yayi ya batawa wani mutumi rai, inda yayi amfani da wayar shi ya dauki bidiyon mai sayar da karas din a lokacin da yake wanke karas din a cikin kwatar.

Mutumin dai ya dauki wannan bidiyo ne domin ya gargadi mutane da suke siyan irin wannan karas akan abubuwan da suke ci.

KU KARANTA: Tirkashi: Rikici ya barke yayin da matar wani limami ta gano cewa yayi sabuwar amarya ba tare da ya sanar da ita ba

A jikin bidiyon an nuno lokacin da mutumin yake amfani da ruwan kwatar yana wanke karas din, yayin da a can daga gefe kuma aka nuno wani mutumi shi kuma yana yin fitsari a cikin kwatar.

Wannan rahoto dai tamkar gargadi ne ga mutane da su lura da irin abubuwan da suke saya, musamman ga mutane masu sayar da kaya irin nan wannan mutumi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel