Tirkashi: Rikici ya barke yayin da matar fasto ta gano cewa yayi sabuwar amarya ba tare da ya sanar da ita ba

Tirkashi: Rikici ya barke yayin da matar fasto ta gano cewa yayi sabuwar amarya ba tare da ya sanar da ita ba

- Asirin wani limamin coci ya tonu bayan yaje ya shirya yin sabon aure a jihar Legas ba tare da ya sanar da uwargidanshi ba

- An bayyana cewa Faston ua baro matar shi a jihar Ogun ya gudo jihar Legas domin ya auri wata mata, sai dai kuma lamarin bai yi musu dadi ba bayan uwargidan ta samu labari

- Uwargidan ta shiga har wajen daurin auren ta ci musu mutunci daga shi har amaryar ta shi ta fice abin ta

Wani lamari da ya faru a ranar Asabar dinnan a jihar Legas ya zama tamkar cin amana, yayin da wani limamin coci mai suna Pastor Olusegun Taiwo ya bar matar shi Vicky a jihar Ogun ya gudu ya je ya auri wata mata daban ba tare da ya sanar da matar tashi ba.

An bayyana cewa anyi bikin Faston da amaryar ta shi mai suna Pastor Wonder, a wata coci mai suna Triumphant, wacce ke a lamba 6 Mathew Ojo Street kusa da governor's road, Ikotun jihar Legas.

KU KARANTA: An kori wata daliba daga makaranta a kasar Saudiyya saboda yanayin halittar da Allah yayi mata

Faston wanda yake zaune a yankin Ijoko dake jihar Ogun, ya shirya auren na shi a jihar Legas din saboda baya so matar shi ta sani. Amma sai dai kuma an sanar da matar ta shi halin da ake ciki, inda tayi tattaki taje har wajen bikin auren nasu ta ci musu mutunci shi da amaryar ta shi ta fita ta wuce abin ta.

An bayyana cewa Faston da ma irin mazan nan ne masu auri saki, tun kafin ya auri uwargidan ta shi dama yana da 'ya'ya guda shida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel