Mutane da dama sun jikkata, an fasa shaguna yayinda yan sandan SARS da mazauna wani yanki suka kara a jihar Taraba

Mutane da dama sun jikkata, an fasa shaguna yayinda yan sandan SARS da mazauna wani yanki suka kara a jihar Taraba

Jami'an rundunar 'yan sanda ta musamman mai yaki da fashi da makami reshen jihar Taraba a jiya Talata, 22 ga watan Oktoba, ta raunana mazauna yankin Mile 6, wani anki a Jalingo, babbar birnin jihar da dama, sannan ta lalata shaguna da sauran cibiyoyin kasuwanci a yankin, jaridar Sun ta ruwaito.

Wani idon shaida, Mista Bitrus Kumai, ya fada ma majiyarmu cewa sun jiyo harbin bindiga ba kakkautawa a safiyar ranar sannan daga bisani sai suka gano cewa jami’an yan sandan SARS ne suka zo sannan suka fara harbi.

Kumai ya bayyana cewa yan sandan sun kuma lallasa duk wanda suka gani yayinda suke lalata shaguna,mashaya da wasu wuraren kasuwanci da dama a yankin.

Mista Thomas Audu, wani mai shagon siyar da kayayyaki, yayi korafin fasa masa shago yayinda tawaga suka shigo a lokacin da yake kula kwastamomi, sannan suka lalata shagon baki daya.

Audu wanda ya nuna raunukan da ya samu daga dukan da aka masa, yayi kiyasin cewa barnar da aka yi masa a shago ya kai N300,000. Ya roki gwamnatin jihar da ta shiga lamarin domin hana sake afkuwar hakan.

Haka zalika, Misis Blessing Aboki, wata mai siyar da bukutu, wacce tawagar yan sandan suka lallasa, ta tuna halin da ta shiga, kama daga lalata mata tukwanenta zuwa ga bari kwastamomi su tsere da kudinta. Tayi ikirarin cewa tayi asarar N80,000.

Mazauna yankin sun ce a baya an kama mutane hudu yayinda aka sake kama wasu uku a ranar sannan cewa har yanzu tawagar na sintiri a yankin.

KU KARANTA KUMA: Kuna da damar sauya sheka, Sule Lamido ga fada ma mambobin PDP

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar, David Misal, wanda ya tabbatar da lamarin, ya bayyana cewa matasa a yankin sun tara kansu domin hana kama wasu guggun yan ta’adda a yankin wanda hakan yayi sanadiyar arangamar da aka yi. Sai dai kuma ya kara da cewa komai ya koma yadda yake a yankin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel