Kuna da damar sauya sheka, Sule Lamido ya fada ma mambobin PDP

Kuna da damar sauya sheka, Sule Lamido ya fada ma mambobin PDP

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, yace babu dole a wajen kasancewa mamba na wani jam’iyya domin kowa na da damar tsallakawa zuwa duk inda yake muradi.

Tsohon gwamnan, wanda ya bayyana hakan a jiya Talata, 22 ga watan Oktoba, yayinda ake jawabi ga mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Dutse, babbar birnin jihar, yace an shirya ganawar ne domin dinke gibin da aka samu a shugabancin jam’iyyar sakamakon sauya sheka ko mutuwa a matakan reshen jihar da karamar hukuma.

Ya bayyana cewa wadanda suka sauya sheka don kawai jam’iyyar ta fadi a zaben da ya gabata, za su gane kwanan nan cewa PDP ce kadai jam’iyyar siyasa da ta cancanci a mace mata a kasar.

Ya kara da cewa da dama, ciki harda shugabannin da suka gabata sun bar jam’iyyar amma duk da haka, jam’iyyar ta rayu, inda ya kara da cewa hakan alama ce dake nuna karara cewa an gina jam’iyyar ne akan ra’ayin kasa da mutane.

KU KARANTA KUMA: Karancin albashi: Kungiyar kwadago ta bukaci gwamnatin tarayya ta biya na watanni 5 da suka gabata

Lamido ya cigaba da bayanin cewa PDP jam’iyyar siyasa ce da aka kafa domin ta rayu ba tare da wadanda ake kia masu karfin iko ba, inda ya kara da cewa bata damu daw a ya bar jam’iyya ba saboda barinsu ba zai sauya komai ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel