Dubu ta cika: Sojoji sun yi ram da wani mai cinikin makamai a Kaduna, sun kama AK 47 guda 6

Dubu ta cika: Sojoji sun yi ram da wani mai cinikin makamai a Kaduna, sun kama AK 47 guda 6

Dakarun rundunar Operation Thunder Strike sun kama wani rikakken mai cinikin makamai a kauyen Sabongaya cikin karamar hukumar Chikun na jahar Kaduna, inda suka kwace bindiga kirar AK 47 guda 6 daga hannunsa.

Jaridar Blue Print ta bayyana cewa mataimakin daraktan watsa labaru na rundunar Soja ta 1 dake garin Kaduna, Kanal Ezindu Idimah ne ya bayyana haka a ranar Talata, 22 ga watan Oktoba, inda yace sun kama mutumin ne yayin da yake kokarin bayar da hayar bindigarsa.

KU KARANTA: An tsinci gawar hafsan Sojan Najeriya a babban birnin tarayya Abuja

“A kokarinmu na kawar da miyagu daga babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, Sojojin Operation Thunder Strike sun kama wani gagararren mai sana’ar sayar da makamai ga yan bindiga da masu garkuwa da mutane a Kaduna.

“Bayan samu tare da tattara ingantattun bayanai, Sojoji sun bi sawun mutumin mai suna Alhaji Shehu zuwa gidansa dake Sabon gaya cikin karamar hukumar Chikun inda muka gudanar da bincike a gidan muka gano bindigu AK 47 guda 6.

“Sai dai Alhaji Shehu yayi ikirarin cewa bindiga guda daya ne kawai nasa, yayin da sauran guda biya kuwa dansa, kaninsa da surukansa ne suka ajiyesu, a yanzu dai mun bazama farautar sauran mutanen dake da hannu cikin sana’ar.” Inji shi.

A wani labarin kuma, Sojoji sun kama wani mutumi mai suna Kamilu Lawal yayin da yake kokarin karbar hayar bindigar wani matashi dan sa kai domin ya yi aikin satar mutane da ita, inda ya yi alkawarin biyansa kudi N150,000.

Daga karshe Kanal Ezindu yace zasu mika mutanen biyu ga hannun Yansanda domin gudanar da bincike a kansu, sa’annan ya bada tabbacin manufar rundunar Sojin Najeriya na yaki da dukkanin miyagun laifuka a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel