Duk da gwamnati bata zo kansu ba, wasu malamai sun rufe gidajensu na horarwa

Duk da gwamnati bata zo kansu ba, wasu malamai sun rufe gidajensu na horarwa

- Bayan bankado makarantun horarwa da azbatarwa tare da barnar da suka zabgawa ga daliban ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada damar bincikosu tare da rufesu

- Makarantun horarwa na jihar Kano kuwa basu jira a zo kansu ba, tuni suka garkame makarantunsu tare da sallamar daliban

- Akwai makarantar da tayi karni biyu da kafuwa a cikin birnin Kanon amma malaman ya sallami daliban gudun fushin hukuma

Bayan hukumomi sun rufe gidajen horarwa a jihohin Katsina da Kaduna tare da gurfanar da malamansu gaban kuliya, masu ire-iren gidajen nan a jihar Kano sun yi wa kansu fada.

Tuni suka sallami dalibansu tare da rufe gidajen don gudun fuskantar fushin hukuma.

Mai tsohuwar makarantar horarwa da ke Sharifai a cikin birnin Kano, Ibrahim Alhajiji, ya ce, miyagun labaran da ke isowa daga jihohin Katsina da Kaduna ne suka sa ya rufe makarantarsa.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun tarwatsa kauyuka 17 a jihar Kaduna

"An kirkiro da makarantar nan ne sama da karni biyu da suka wuce. Ana gyara yara fiyeda 1000 tare da basu ilimin addinin Islama. Rufe makarantar babban kalubale ce garemu malaman da kuma iyayen yaran. Suna ta kiranmu da mu kara duba lamarin," Alhajiji ya sanar da jaridar Premium Times.

Ya ce, kafin rufe makarantar, akwai dalibai 70 'yan Najeriya, Nijar da kasar Kamaru.

Amma kuma wakilin Premium Times ya ce, ya lura akwai dalibai da ke ta karatun Qur'ani a farfajiyar makarantar amma kuma ba daure suke ba. An sanar dashi cewa, saboda basu da taurin kai ko rashin jin magana ne yasa hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel