Majalisa za ta goyi bayan EFCC da ICPC wurin yakar cin-hanci – Sanata Lawan

Majalisa za ta goyi bayan EFCC da ICPC wurin yakar cin-hanci – Sanata Lawan

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Lawan Ahmad a ranar Talata 22 ga watan Oktoba ya ce majalisa za ta bai wa hukumomin yaki da cin hanci goyon baya wurin kawar da matsalar cin-hanci a Najeriya.

Lawan ya ce hukumomin EFCC da ICPC su ne kan gaba a wurin yaki da cin-hancin yayin da wasu makamantansu ke biye da su a baya. Ya kuma majalisar dokokin gaba dayanta a shirye take domin goyon bayan fada da cin-hancin.

KU KARANTA:Ezra Suwanta Zako: Mutum mafi tsawo a jihar Kaduna (Hotuna)

Mai magana da yawun Shugaban majalisar dattawan, Mr Ola Awoniyi ne ya fitar da wannan zancen daga cikin jawabin Sanata Lawan a wurin wani taron EFCC da akayi a Abuja.

Sanatan ya ce: “Matsalar da muke fuskanta a kasar nan bangaren cin-hanci babbar matsala ce wadda ke bukatar hadin kai.

“A shirye muke da yin aiki da sauran sassan gwamnati domin fada da cin-hanci. Fada da dole kowa sai ya sanya hannunsa a cikin har mu ga mun yi nasara.

“Hukumomin EFCC da ICPC za su cigaba da samun goyon bayanmu wurin tabbatar da an yi nasara a yaki da cin-hanci.” Inji Lawan.

Haka zalika, Sanatan ya kara da cewa, cin-hanci ya yiwa kasar nan illa matuka. Haka kuma ya sake cewa gwamnatin Shugaba Buhari a cikin ‘yan shekarun nan tayi kokari wurin fada da cin-hancin.

“Yaki da cin-hanci ya shafi kowa da kowa, a don haka alkalai da ‘yan sanda sun shiga cikin wannan tafiya, har sai mun cinma burinmu na kawar da cin-hanci a kasar nan". Inji Lawan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel