An tsinci gawar hafsan Sojan Najeriya a babban birnin tarayya Abuja

An tsinci gawar hafsan Sojan Najeriya a babban birnin tarayya Abuja

Hankula sun tashi yayin da aka gano gawar wani hafsan Sojan kasa a daidai gefen gadar Mabushi ta hanyar shiga Utako dake cikin babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda rahoton jaridar Premium Times ya bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an tsinci gawar hafsan Sojan mai suna VL Henry kuma mai mukamin Second Liutenant kamar yadda katin shaidarsa ta nuna ne da misalin karfe 8:40 na safiyar talata, 22 ga watan Oktoba.

KU KARANTA: Tsautsayi: Injin nika ya kwashe ma wani yaro y’ay’an maraina a jahar Bauchi

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa akwai alamun sara da raunuka a kansa, sai dai duk kokarin da majiyar ta yi na jin ta bakin kaakakin rundunar Sojan kasa bai yiwu ba sakamakon baya daukan wayansa.

Sai dai wasu Sojoji da suka nemi a sakaya sunansu sun bayyana cewa kashe Sojan aka yi, kuma daga dukkan alamu rikici ne ya hadashi da wasu mutane da ba’a san ko su wanene ba suka yi masa wannan kisan gillar.

Wanna kisa na Henry yazo ne bayan kwanaki kadan da dawowarsa daga garin Calabar inda ya halarci wani kwas, kuma Sojan yana aiki ne a rundunar Soja ta 3 dake garin Jos, tuni aka mika gawarsa zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Abuja.

Wannan kisa ta kara tabbatar da matsalar rashin tsaro dake neman mamaye babban birnin tarayya Abuja, inda a yan kwanakin nan ake yawan samun rahoton hare haren yan bindiga, satar mutane, da kuma fashi da makami.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel