Ba mu da labari game da kai wa Kwankwaso hari a Kano – Yan sanda

Ba mu da labari game da kai wa Kwankwaso hari a Kano – Yan sanda

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano, ta ce ba ta samu bayani ba akan zargin da tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi na cewa harin da aka kai musu an shirya shi ne daga gidan gwamnatin jihar.

A cewar rundunar 'yan sandan jihar, ko da wasa ba ta da masaniyar rikicin da bangaren Kwankwasiyya suka yi zargin ya afku.

Kakakin rundunar ta jihar, DSP Haruna Abdullahi ya ce "An kira mu domin mu je Madobi, kuma mun tura jami'anmu amma ba su ga wani abu na faruwa ba."

Ya kara da cewa "babu wani korafi da muka samu a rubuce balle ma har mu yi bincike saboda haka idan mutum yana da korafi to ya rubuta mana sai mu gudanar da bincike a kai."

KU KARANTA KUMA: Zan yi amfani da iyayen yan daban siyasa mata don kare akwatunan zabe a Kogi – Zahrah Mustapha Audu

A baya mun ji cewa tsohon Sanata kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso, ya gwamnatin jihar Kano a karkashin jagorancin gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ita ce ta kitsa harin da aka kai wa tawagarsa da yammacin ranar Litinin a cikin garin Kano.

An kai wa Kwankwaso da tawagarsa harin ne a daidai gadar Sabon Titin Panshekara yayin da suke dawowa daga kauyen Kwankwaso da ke karkashin karamar hukumar Madobi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel