Har ila yau: An samu yara uku a daure da sarka a wani haramtaccen gidan horo a Zaria

Har ila yau: An samu yara uku a daure da sarka a wani haramtaccen gidan horo a Zaria

Jami'an hukumar tsaro ta NSCDC, wacce aka fi sani da 'Civil Defence', sun kara kai samame wani haramtaccen gidan horo tare da kubutar da mutane 11 a garin Zariya, Jihar Kaduna.

Ma'aikatan sun kai samamen ne da misalin karfe 8:00 na safiyar ranar Talata, inda suka yi awon gaba da malamai 11 da ke cibiyar.

A rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa, ta ce jami'an na 'Civil defence' sun samu wasu daga cikin wadanda ake azabtarwa a cibiyar a daure da sarka.

An saka wa haramtacciyar cibiyar suna 'Makarantar Malam Aliyu Mai Adaka', kuma tana unguwar Limanci, daya daga cikin tsofin unguwannin asalin garin Zazzau.

A cewar Daily Trust, wasu daga cikin fursunonin cibiyar suna da tabin hankali, kuma saboda hakan ne aka daure su da sarka kafin jami'an NSCDC su kubutar da su.

Wakilin Daily Trust ya ce manya daga cikin fursunonin suna cikin yanayin tsananin rama, lamarin da ke nuni da cewa suna fama da yunwa ga kuma kuraje a jikinsu.

Da yake bajakolin wadanda ake zargi da mallakar cibiyar a Kaduna, mataimakin kwamandan rundunar NSCDC, Nnegha Onyema, ya ce zasu mika fursunonin ga gwamnatin jihar Kaduna ta hannun ma'aikatar jin dadi da walwalar jama'a sannan su cigaba da gudanar da bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel