Kulle iyakoki: Kamfanin kayen mayen 'Alomo Bitters' ta yi asarar $2m

Kulle iyakoki: Kamfanin kayen mayen 'Alomo Bitters' ta yi asarar $2m

Kamfanin Kasapreko Company Limited dake kasar Ghana ne masu shigo da shahrarriyar kayen mayen "Alomo Bitters" da yan Najeriya suke sha.

Kamfanin ta yi asarar dala milyan biyu tun lokacin da gwamnatin Najeriya ta kulle iyakokinta.

Wannan labari ya bayyana daga bakin babban jami'in kamfanin, Francis Holly Adzah, a hirar da yayi da jaridar kasar Ghana, JoyBusiness, cewa sun yi asarar $2million sakamakon rufe boda.

Kamfanin kayen mayen ta ce motoci uku kawai suka samu shigowa Najeriya kafin kulle bodan.

Ya ce akwai motoci hudu yanzu makare da kaya amma babu hanyar shigowa da su Najeriya.

Adzah yace: "A watan Satumba, mun yi asaran $1 million sakamakon rufe iyakar. Gashi watan Oktoba ya zo karshe kuma hasashe ya nuna cewa mun sake asarar dala milyan daya. Abinda ya fara tada mana da hankali."

Wannan abu ya tilasta kamfanin fara tura kaya wasu kasashen Afrika irinsu Ivory Coast, Senegal, Togo, Benin da wasu kasashen Turai domin rage zafi.

A bangare guda, Kungiyar 'Yan kasuwa na Ghana (GUTA) sun yi kira ga mambobinsu su kauracewa kayayyakin da ake shigarwa kasarsu duba da cewa rufe boda ta Najeriya ya jefa kasashen Afirka ta Yamma cikin mawuyacin hali.

'Yan kasuwan suna sa ran wannan matakin da suka dauka zai tilastawa gwamnatin Najeriya ta bude iyakokin ta na kasa domin a fara shigo da kayayyaki daga kasashen waje. Tun a watan Augusta ne Najeriya ta fara rufe wasu iyakokin na ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel