Yanzu-yanzu: Mun fara bincike a gidan yari na Ikoyi - CG

Yanzu-yanzu: Mun fara bincike a gidan yari na Ikoyi - CG

Ja'afaru Ahmed, Kwantrola Janar na Hukumar Gidan Gyran Hali ta Najeriya, ya ce ya kafa kwamitin binciken a gidan yari na Ikoyi da ke Legas bayan binciken da wani dan jarida, Fisayo Soyombo ta ya yi.

Soyombo ya yi kwanaki takwas a matsayin fursuna a gidan yari na Ikoyi domin ya gano rashawa da ke gudana a gidan yarin.

Ya bayyana abubuwan da ya gano kan matsaloli da suka hada da 'ta'amulli da miyagun kwayoyi, 'luwadi, cin hanci, karuwanci' da sauransu duk dai a gidan yarin.

DUBA WANNAN: Wata budurwa ta fadi aka rika yin zina da su a gidan 'azabtarwa' na Kaduna (Bidiyo)

The Cable ta ruwaito cewa a daren Talata Ahmed ya dukkan wadanda aka samu da hannu cikin aikata laifukan za su fuskanci hukuncin da ya dace da su.

Ku biyo domin karin bayani ...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel