Fasa kauri: Sojin ruwa sun kama mutum 12, sun kwace buhuhunan shinkafa 708

Fasa kauri: Sojin ruwa sun kama mutum 12, sun kwace buhuhunan shinkafa 708

Rundunar sojin ruwa a yankin Ibaka a karamar hukumar Mbo dake jihar Akwa Ibom, ta kama wasu mutane su 12 bisa zargin fasa kaurin shinkafa yar kasar waje, buhuhunan 50kg har guda 708.

Daga cikin mutanen da aka kama harda bebe da kurma wadanda aka kama a jirgin kwale-kwalen da suke anfani dashi wajen fasa kaurin shinkafa, a lokacin da jami’an sojin ruwan ke faturol a sashin hanyoyin ruwan Effiat.

Kwamandan rundunar, FOB, Captain Peter Yilme ya bayyana a Ibaka a lokacin da yake mika masu laifin da kayayyaki zuwa ga hukumar kwastam, cewa masu fasa kwarin na amfani da sabbin hanyoyin shigo da haramtattun kayayyaki domin gujewa kamu, amman cewa rundunar sojin ruwa zata cigaba da dakile haramtattun kasuwanci.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan sanda kama wani dan majalisar Benue

Yace, a lokacin da rundunar sojin ruwa ta kama daya daga cikin kungiyoyin uku, masu laifin sun yi yunkurin haka rami a jirgin ruwan don nutsad da jirgin.

Ya bayyana cewa, kame-amen da ake cigaba da yi ya rage yawan ayyukan fasa kauri, inda ya kara da cewa rundunar na cigaba da maganin yan fashin teku.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel