Yanzu Yanzu: Yan sanda kama wani dan majalisar Benue

Yanzu Yanzu: Yan sanda kama wani dan majalisar Benue

Rahotanni sun kawo cewa yan sanda sun kama Jonathan Agbidye, wani mamba a majalisar dokokin jihar Benue, akan yawan ayyukan ta’addanci a mazabarsa.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Agbidye na wakiltan mazabar Katsina-Ala ta yamma a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wacce ta kasance jam’iyyar adawa a jihar.

An tattaro cewa jami’an tawagar Inspekta Janar na yan sanda ne suka kama dan majalisar sannan suka tafi dashi zuwa Abuja.

An tattaro cewa an kama Agbidye ne biyo bayan wani korafi da mambobin mazabar suka turawa IGP game da zargin hannunsa a ayyukan ta’addanci a yankin.

An yi zargin cewa a lokacin da aka kama dan majalisar, a gano shi daukee da wata motar Toypta Hilux wacce aka ce wasu yan fashi sun kwace daga hannun matar marigayi Justis Tine Tur.

Sai dai kuma, kakakin majalisar dokokin jihar Benue, Titus Uba yace an gayyaci Agbidye ne domin amsa wasu tambayoyi.

KU KARANTA KUMA: Zan yi amfani da iyayen yan daban siyasa mata don kare akwatunan zabe a Kogi – Zahrah Mustapha Audu

Kakakin yan sandan jihar Benue, Catherine Anene, tace bata san da batun kamun ba amma ta tabbatar da kasancewar tawagar IGP a jihar domin aiwatar da ayyuka na musamman.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel