Gwamna Bala Mohammed ya nada Ma’aji Misau shugaban ma’aikatan Bauchi

Gwamna Bala Mohammed ya nada Ma’aji Misau shugaban ma’aikatan Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya aminta da nadin Alhaji Ahmed Abubakar Ma’aji Misau a matsayin shugaban ma’aikatan jihar na rikon kwarya.

Sakataren gwamnatin jihar Bauchi, Alhaji Muhammad Sabi’u Baba ne ya fitar da wannan labarin. Inda ya ce kafin nadin Ma’aji Misau wannan mukamin shi ne babban sakatare mafi dadewa a ma’aikatar jihar Bauchi.

KU KARANTA:A watan Afrilun 2020 za a kammala gyaran filin jirgin Enugu – Sirika

Tun a shekarar 1985 Alhaji Misau ya soma aiki da ma’aikatar jihar Bauchi yayin da a watan Yunin 2016 ne ya samu zama babban sakataren din-din din a ma’aikatar.

A wani labarin kuwa za ku ji cewa, Ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika ya ce zuwa karshen watan Afrilun shekarar 2020 za a kammala aikin gyaran filin jirgin saman Akanu Ibiam na jihar Enugu.

A ranar Talata 22 ga watan Oktoba, 2019 ya ce zai koma da ofishinsa jihar ta Enugu har sai an kammala gyaran filin jirgin. Sirika yayi wannan jawabin ne a gaban kwamitin kula da sufurin jiragen sama na majalisar dokoki, lokacin da yake amsa tambayoyi game da kasafin kudin 2020 na ma’aikatar.

https://www.dailytrust.com.ng/maaji-misau-is-new-bauchi-head-of-service.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel