Yanzu-yanzu: Hukumar yaki da rashawa ta alanta neman tsohon hadimin shugaba Buhari ruwa a jallo

Yanzu-yanzu: Hukumar yaki da rashawa ta alanta neman tsohon hadimin shugaba Buhari ruwa a jallo

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ICPC ta alanta neman tsohon shugaban kwamitin bincike da kwato kudaden sata SPIP, Okoi Obono-Obla.

Hukumar ta bayyana cewa ta dau wannan mataki ne saboda Obono-Obla ya ki bayyana gabanta duk da sammacin da tayi masa domin amsa tambayoyi bisa ga zargin da ake yi masa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami Okoi Obla ne daga watan Agusta zuwa lokacin da hukumar ICPC za ta kammala bincike kan zargin da ake yi masa.

A jawabin da hukumar ta saki ranar Talata, ta ce: "Hukumar ta samu takardun zarge-zarge da ake yi masa na ci da kujera, amfani da takardun bogi, rayuwa sama da abinda yake samu da karban rashawa daga hannun mutanen da ake zargi da laifi."

"Hakazalika yana fuskantar zarge-zargen wuce gona da iri wajen jagorantan kwamitin da aka nada shi ta hanyar binciken wasu kararraki da hukunta wasu ba tare da izinin ofishin babban lauyan tarayya ba."

"ICPC ta gudanar da bincike kuma ta samu cewa Mista Obono Obla ya sabawa dokokin kasa."

Hukumar ta ce an samu tabbataccen rahoton cewa Obono Obla ya arce daga Najeriya tun Agusta kuma har yanzu bai dawo ba.

SHIN KO KA SAN Kano 9: An mika yaran da aka sace zuwa Anambara ga gwamnatin Kano

A bangare guda, Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar Legas ta tsayar da ranar 2 ga watan Disamba domin zartar da hukunci a kan zargin badakala da almundahana da kudin jama'a da hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki ke yi wa tsohon gwamnan jihar Abiya, Sanata Orji Uzor Kalu.

Alkalin kotun, Jastis Mohammed Idris, ya tsayar da ranar yanke hukuncin ne a ranar Talata bayan lauyoyin masu kara da wadanda ake kara sun kammala gabatar da hujjojinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel