‘Dan wasa Ronaldo ya yi wa Mayorga fyade – DNA sun nuna

‘Dan wasa Ronaldo ya yi wa Mayorga fyade – DNA sun nuna

An samu wasu kwayoyin halittar jikin fitaccen ‘Dan wasa Cristiano Ronaldo a jikin Kathryn Mayorga wanda ta ke zargin ‘dan kwallon da laifin yi mata fyade shekaru da su ka wuce.

Kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar The Sun, gwajin da aka yi a wani dakin bincike ya bayyana cewa an samu kwayoyin DNA na Cristiano Ronaldo, wanda ke nuna cewa da walakin.

Jaridar kasar Ingilar ta kuma rahoto cewa Ronaldo ya fadawa Lauyoyinsa duk yadda abin ya faru a karon da ya yi da Kathryn Mayorga a shekarar 2009 a wani gidan caca da ke birnin Las Vegas.

Wani Jami’in da ke binciken lamarin, Jeffrey Guyer ya tabbatar da cewa akwai kwayoyin halittar Ronaldo a jikin wannan Mata da ke zargin ‘dan kwallon Duniyar da tarawa da ita da karfin tsiya.

KU KARANTA: An binciko irin dukiyar da Ronaldo ya ke samu a Instagram

Jeffrey Guyer ya bayyana wannan ne a wani daga cikin sakonnin da ya aikawa hukuma. Jami’in ya rubuta wani dogon bincike na tsawon shafyka 100 inda ya fitar da rahoton abin da ya auku.

Shi dai Ronaldo ya karyata wannan zargi tun lokacin da aka jifesa da shi. ‘Dan wasan na kasar Portugal ya fito gaban Duniya ya musanya wannan ne a shafin sa na sada zumunta na Tuwita.

Mayorga mai shekaru 34 ta na karar Gwarzon ‘dan kwallon ne inda ta ke neman a biya ta fam £165,000 na ci mata zarafi. A cewar ta Ronaldo ya bi ta cikin kewaye ne inda ya fito mata a mutum.

Kwanaki Miss Mayorga ta ba ‘yan jarida labarin yadda su ka hadu da Ronaldo da ‘dan uwansa wajen wani biki. Jami’an Garin Nevada sun ki gurfanar da Ronaldo domin a binciki wannan zargi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel