Kwastam sun gano wani gida da ake canjawa shinkafa buhu, sun kama mutum 15 (Hoto)

Kwastam sun gano wani gida da ake canjawa shinkafa buhu, sun kama mutum 15 (Hoto)

Rundunar hukumar Kwastam na jihohin Adamawa/Taraba, NCS, ta ce jami'an ta sun kama mutane 15 da ake zargi da canjawa shinkafar kasan waje buhu suna sayar da ita a matsayin shinkafar gida Najeriya.

Kwantrollan hukumar mai kula da jihohin Adamawa/Taraba, Kamardeen Olumoh ya shaidawa manema labarai a ranar Talata cewa an koma wadanda ake zargi 15 din ne a wani gidan ajiyar kaya a Yola.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Mista Olumoh ya ce an same su buhunnan shinkafa 900 da ya kamata a biya musu haraji na naira miliyan 14.5.

Kwastam sun gano wani gida da ake canjawa shinkafa buhu, sun kama mutum 15
Kwastam sun gano wani gida da ake canjawa shinkafa buhu, sun kama mutum 15
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wata budurwa ta fadi aka rika yin zina da su a gidan 'azabtarwa' na Kaduna (Bidiyo)

Olumoh ya ce, "Mun kama mutane 15 da muke zargi cikinsu har da mai gidan ajiyar kayayakin da wasu leburori.

"Muna tabbatar muku cewa za a hukunta su kamar yadda doka ta tanada."

Olumoh ya gargadi masu fasakwabrin kayayaki a garin da su dena domin hukumar ba za ta ragawa duk wanda aka kama ba.

Ya ce nan ba da dadewa ba jami'an hukumar za su fara zuwa kasuwanni don kama shinkafar kasashen waje.

Ya ce, "Munyi taro da 'yan kasuwan Yola mun gargadi su kan su dena sayar da shinkafar kasashen waje.

"Dole mu taimakawa manoman mu na Najeriya saboda na tabbatar za su iya ciyar da kasar."

Kwantrollan ya nuna wa manema labaran wata babbar mota da aka kama dauke da shinkafar kasar wahe a kan hanyar Mubi zuwa Yola dauke da buhunnan wake da wasu hatsi da ya dace a biya musu kudin haraji naira miliyan 10.3.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel