Badakalar N7bn: Kotu za ta zartar da hukunci akan Orji Kalu bayan shakara 12

Badakalar N7bn: Kotu za ta zartar da hukunci akan Orji Kalu bayan shakara 12

Wata babbar kotun tarayya da ke Lagas ta sanya ranar 2 ga watan Disamba domin yanke hukunci akan shari’an Orji Uzor Kalu, tsohon gwamnan jihar Abia.

Alkalin kotun, Mohammed Idris, ya tsayar da ranar ne a yau Talata, 22 ga watan Oktoba, bayan lauyoyin sun gabatar da rubutattun jawabansu na karshe.

Hukumarr yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ce ta gurfanar da Kalu tare da Slok Nigeria Limited, kamfaninsa da kuma Udeh Udeogu, daraktan kudi da asusunsa yayinda yake a matsayin gwamna, akan tuhume-tuhume 39 na wawure kudi har naira biliyan 7.6.

An fara shari’an ne tun a 2007, amma bai samu kammaluwa ba.

Baya ga naira biliyan 7.6, wanda ake zarginsa da karkatarwa, ana kuma zargin wanda ake karan da karban naira miliyan 460 daga baitun malin gwamnatin jihar Abia a tsakanin watan Yuli da Disamba 2002.

KU KARANTA KUMA: Badakalar N25bn: Kotu ta bukaci ICPC ta kawo mata ministan Buhari

Lauyan mai kara ya kira shaidu 19, yayinda wadanda ake karar suka kare kansu.

A yanzu haka Kalu ya kasancee Sanata mai wakiltan yankin Abia ta tare.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel