Zan yi amfani da iyayen yan daban siyasa mata don kare akwatunan zabe a Kogi – Zahrah Mustapha Audu

Zan yi amfani da iyayen yan daban siyasa mata don kare akwatunan zabe a Kogi – Zahrah Mustapha Audu

Uwagidar dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kogi, Princess Zahrah Mustapha Audu, ta bayyana cewa za ta tattara iyayen yan daban siyasa a kananan hukumomi 21 dake jihar domin tabbatar da zabe cikin lumana a ranar 16 ga watan Nuwamba.

Da take magana akan kokawar da hukumar zabe mai kanta (INEC) tayi game da yiwuwar barkewar rikici a Kogi a lokacin zaben gwamna, tace za a kwashi iyayen yan daban siyasa mata domin su kare mazabu a lokacin zabe.

A wani hira a Abuja, ta bayyana shirinta na jagorantar wata tawaga ta mata domin kula da mazabu a jihar, cewa ya zama dole ayi zabe a gaskiya da amana a jihar Kogi.

"Akwai matsaloli a jihar Kogi oda dai burina ne ganin APC ta cigaba da shugabancin jihar. Burina ne ganin gwamnanmu mai ci, wanda ya kasance dan takararmu, ya cigaba da kuma kammala mulkinsa amma ba wai ta yadda rayuka da dukiyoyin mutanen jihar Kogi za su salwanta ba," inji ta.

Surukar ta marigayi Abubakar Audu, ta bukaci gwamnan jihar, Yahaya Bello da ya dakatar da kamfen dinsa a kananan hukumomi 21 na jihar, cewa ba dabara bane yin abunda zai zamo barazana ga damar jam’iyyar a jihar.

KU KARANTA KUMA: Badakalar N7bn: Kotu za ta zartar da hukunci akan Orji Kalu bayan shakara 12

A baya mun ji cewa sashen TEI da ke karkashin hhukumar INEC mai zaman kanta, ta kyankyasa cewa alamun farko sun gama nuna cewa za a samu rikici wajen zaben gwamnan jihar Kogi da ake shirin gudanarwa.

Shugaban TEI, Prince Solomon Adedeji Soyebi, ya bayyana wannan a lokacin da aka shriya wani zama game da zaben na jihar Kogi. An yi wannan zama ne a Garin Abuja a Ranar 21 ga Oktoba.

Prince Solomon Adedeji Soyebi ya kuma nuna cewa an fara shirin sayen kuri’un jama’a ban da tanadin rigimar da ake yi. Shugaban sashen ya yi albishiri cewa za su takawa shirin burki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel