A watan Afrilun 2020 za a kammala gyaran filin jirgin Enugu – Sirika

A watan Afrilun 2020 za a kammala gyaran filin jirgin Enugu – Sirika

Ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika a ranar Talata 22 ga watan Oktoba ya ce zai mayar da ofishin zuwa filin sauka da tashin jirage na Akanu Ibiam dake Enugu na wucen gadi.

Sirika ya ce zai koma Enugun ne domin tabbatar da an kammala gyaran filin jirgin zuwa watan Afrilun 2020. Haka kuma ministan ya bayyana cewa aikin da ake yi a filayen jirgin Aminu Kano da Murtala Mohammed na Legas zuwa karshe shekara za a gama.

KU KARANTA:Yanzu-yanzu: Makusantan Jonathan sun fice daga PDP zuwa APC

Ministan ya fadi wannan maganar ne a gaban kwamitin majalisa mai kula da lamuran sufurin jirgin sama, a yayin da yake amsa tambayoyi game da kasafin kudin ma’aikatarsa.

Ministan ya bayar da tabbacin cewa, da N10bn da Shugaban kasa ya bayar domin gyaran filin jirgin Enugu ma’aikata za su fara aiki ba tare da bata lokaci ba. Ya kuma kara da cewa bayan an kammala gyaran, filin jirgin zai kasance mafi kyawo kasar gaba daya.

Sirika ya sake cewa, mutanen da gidajendu ke makwabtaka da filin jirgin za su tashi saboda su hutu da takura na sauka da tashin jiragen.

Da kuma yake amsa tambaya game da tsaftar filayen jirgin saman Najeriya. Ministan ya ce, a cikin filayen jirgi 22 da suke kasar 21 duk tsaftatattu ne in banda guda daya kacal. Wannan kuma shi ne na Legas.

A lokacin da aka gina filin jirgin an yi shi ne domin mutane 200,000 kacal amma a yanzu kuwa yana samun mutane kimanin miliyan 8, a cewar Sirika.

https://thenationonlineng.net/enugu-airport-to-be-ready-by-april-2020-hadi-sirika/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel