Tirkashi: Wani saurayi ya sha alwashin kashe dan gidan shugaban kasar Amurka Donald Trump

Tirkashi: Wani saurayi ya sha alwashin kashe dan gidan shugaban kasar Amurka Donald Trump

- An tisa keyar wani saurayi mai suna Chase Bliss Colasurdo zuwa gidan kurkuku, bayan an kama shi da wani laifi

- An cafke Chase ne bisa laifin yunkurin kashe dan gidan shugaban kasar Amurka Donald Trump da kuma surukinsa Jared Kushner

- Haka kuma Chase ya wallafa wani rubutu a shafinsa dake nuni sa cewar ya shirya kaiwa wuraren bauta na kasar Amurka hari

Wani saurayi dan shekara 27 mai suna Chase Bliss Colasurdo, an yanke masa hukuncin shekara biyar a gidan kaso bayan kama shi da laifin yunkurin kashe dan gidan shugaban kasar Amurka Donald Trump Jr, da kuma surukinsa mai suna Jared Kushner.

Chase wanda dama yana da tabin hankali, hukumar 'yan sandan farin kaya ta cafke shi bayan ya wallafa wani hoto inda ya sanya bakin bindiga akan sirikin shugaban kasar Jared Kushner, da kuma shan alwashin kashe dan gidan shugaban kasar Donald Trump Jr.

Haka kuma Chase ya wallafa barazana da yawa shafukansa na sada zumunta, inda ya wallafa cewa zai kaiwa wuraren da ake gabatar da bauta hari.

KU KARANTA: Kwankwaso zai kara daukar nauyin yaran talakawa zuwa kasashen turai domin karo ilimi a jihar Katsina

Chase dai ya sayi harsashi, da rigar dake kare harbin bindiga, amma kuma an hana shi sayen bindiga yayin da hankalin hukumar 'yan sandan farin kayan ta kai kanshi.

Yanzu haka dai an yankewa Chase hukuncin shekara biyar a gidan kaso bayan an same shi da laifi akan duka abubuwan da ake tuhumar shi a kai. Lauyan shi dai ya roki kotu da ta rage shekarun zuwa shekara daya, sannan ta sanya a tsare shi a gida na tsawon shekara biyar, sai dai kotun tayi watsi da wannan bukata ta lauyan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel