Jami’an Road Safety sun kashe mutumin daya hanasu cin hanci, sun boye gawarsa a Edo

Jami’an Road Safety sun kashe mutumin daya hanasu cin hanci, sun boye gawarsa a Edo

Wasu baragurbin jami’an hukumar kare haddura ta kasa, FRSC, dake aiki a ofishinsu na Abudu jahar Edo sun kashe wani bawan Allah mai suna Odion Samuel sa’annan suka binneshi cikin wani kabari mara zurfi, inji rahoton jaridar Sahara Reporters.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito sunayen jami’an da suka aikata wannan aika aika kamar haka, Francis Igoh, Sunday Ogi, Samson Alolade da kuma Joseph Onolade, kuma sun kashe Odion ne saboda ya hanasu karbar cin hanci da rashawa daga hannun wani direba.

KU KARANTA: Ajali ya yi kira: Ruwan kududdufi ya cinye wani mutumi dan shekara 40 a jahar Kano

Wannan mummunan lamari ya auku ne a ranar 14 ga watan Oktoba a kusa da tsaunin Okhuaihe dake kan babbar hanyar Bini zuwa Agbor, inda da fara jami’an suka fara tsare motar tare da tuhumar direban motar da sacewa da kuma yin garkuwa da Odion.

Sai dai daga bisani binciken Yansanda ya nuna cewa jami’an FRSC ne suka kashe Odion, bayan sun sha dan karan tambaya daga wajen Yansanda sai suka garzaya da Yansanda zuwa inda suka binne gawar mamacin.

Kaakakin Yansandan jahar Edo, DSP Chidi Nwabuzor ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana lamarin a matsayin laifin kisan kai da gangan, sa’annan yace zasu gurfanar da mutanen biyu gaban kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel