Yanzu-yanzu: Makusantan Jonathan sun fice daga PDP zuwa APC

Yanzu-yanzu: Makusantan Jonathan sun fice daga PDP zuwa APC

Wadansu makusantan tsohon Shugaban kasar najeriya Goodluck Jonathan sun fice daga PDP zuwa APC. Wadannan mutanen dai sun hada da, Cif Enogha Robert da Cif Claudius Enegesi.

Mutanen dai sun sauya sheka ne zuwa APC a sakamakon zaben gwamnan jihar dake tafe a ranar 16 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA:NYSC za ta gina gidan rediyo na miliyoyin kudi a Abuja

Enogha ya taba rike mukamin kwamishinan muhalli na jihar Bayelsa. Haka kuma yana daya daga cikin manyan mutane masu fada a ji a karamar hukumar Ogbia dake jihar.

Enegesi kuwa na hannun daman Jonathan ne sosai, wanda ya taba rike mukamin Kakakin majalisar tsohuwar jihar Rivers, a lokacin da Ada George yake gwamnan jihar.

Haka zalika shi ne shugaban jam’iyyar PDP na farko a Bayelsa yayin da aka kafa ta a shekarar 1998. Kuma ya daya daga cikin jiga-jigan PDP a karamar hukumar Ogbia.

Bugu da kari a karamar hukumar Nembe, akwai Cif Bright Erewari-Igbeta wanda shi ma ya sauya sheka zuwa APC. Bright tsohon dan majalisar jihar Bayelsa ne kuma a yanzu haka shi ke baiwa gwamnan jihar shawara game da muhalli.

Labarin da muka samu daga majiyar The Nation shi ne, Bright ya ajiye mukaminsa kuma ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Har ila yau, akwai Cif James Jephathah wanda aki sani da Octopus, shi ma ya ce babu shi ba PDP. Kamar yadda Octopus ya fadi, da shi da magoyan bayansa duk sun raba jaha da PDP.

https://thenationonlineng.net/just-in-jonathan-kinsmen-others-dump-pdp-for-apc/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel