Yanzu-yanzu: An kashe mutum 7, an kone gidaje da dama sakamakon barkewar rikici a Okundi

Yanzu-yanzu: An kashe mutum 7, an kone gidaje da dama sakamakon barkewar rikici a Okundi

A kalla mutane bakwai ne suka rasa rayyukansu yayin da aka kone gidaje masu yawa sakamakon barkewar rikicin kungiyoyin 'yan daba a garin Okundi a karamar hukumar Boki na jihar Cross Rivers a safiyar ranar Talata.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa rikicin ya barke ne bayan an kashe wani matashi mai suna Joseph Bankong, a garin a daren ranar Litinin wanda ya ke kokarin yaki da masu neman kafa kungiyoyin asiri.

Wani mazaunin kauyen wanda lamarin ya faru a idanunsa, ya ce, "Kissar gillar da aka yi wa Bankong ne ya saka dukkan 'yan garin suka sha alwashin daukan fansa kan wadanda ake zargin 'yan kungiyan asiri ne.

DUBA WANNAN: Wata budurwa ta fadi aka rika yin zina da su a gidan 'azabtarwa' na Kaduna (Bidiyo)

"Yayin rikicin an kashe Alphonsus Etta Ewung, Otu Agbor Edum, da 'dan Cif Paulinus Otu."

Kwamishinan rundunar 'yan sanda na jihar, Austin Agbonlahor ya tabbatar da afkuwar lamarin. Ya kara da cewa "'yan sanda sun isa wurin yanzu domin kwantar da tarzomar".

A wani rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa Sashin warware bama-bamai na rundunar 'yan sandan Najeriya (EOD) ta ce ta gano wani bam da aka saka a harabar Hukumar zabe mai zaman kanta INEC na garin Owerri a jihar Imo.

The Punch ta ruwaito cewa rundunar ta ce an kai bam din samfurin 80mm zuwa hedkwatan na EOD a jihar inda ta ce an kuma gano wasu bama-baman uku a harabar kamfanin siminti na BUA da ke Okpella a jihar Edo a ranar 1 ga watan Oktoban 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel