Ko daya ba mu katange ‘yan jarida daga shiga sauraron kare kasafin kudi ba - Lawan

Ko daya ba mu katange ‘yan jarida daga shiga sauraron kare kasafin kudi ba - Lawan

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmed Lawan ya yi watsi da rade-radin cewa majalisar ta hana manema labarai shiga zaman sauraren muhawarar kare kasafin kudi wanda ke cigaba da gudana a zauren majalisar.

A yayinda yake mayar da martani ga rahotannin da wasu kafafen yada labarai suka wallafa, mai magana da yawun Lawan, Ola Awoniyi, yace ko daya bah aka lamarin yake ba. Yace babu wanda ya hana manema labarai shiga zauren muhawaran.

Wasu kafafen yada labarai dai sun ruwaito cewa an hana manema labarai shiga sauraren kare kasafin kudin, wanda ake kiran shugabannin bangarori domin kowa ya kare kasafin kudin sa.

“Ba mu hana manema labarai shiga sauraren dukkan abin da mu ke yi ba.

“Ai mu na ma bukatar manema labarai domin su rika sanar wa ‘yan Najeriya abin da mu ke yi a majalisa. Ku ‘yan jarida ai abokan mu ne. Da aka ce mun hana ku shiga, ba daidai ba ne.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kalli yadda rundunar sojin sama ta tayar da mafakar yan ta’adda a Borno, ta kashe mayakan Boko Haram da dama (bidiyo)

Sai dai kuma Lawan din ya ce amma abin lura a nan shi ne, akwai wasu batutuwan da ke bukatar sirri, musamman idan sun shafi abin da ke bukatar sirrantawa a kasar nan, saboda wasu dalilai, kamar na tsaro, to shi ne sai a nemi uziri daga manema labarai.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel