'Yan sanda sun gano bama-bamai a harabar ofishin INEC

'Yan sanda sun gano bama-bamai a harabar ofishin INEC

Sashin warware bama-bamai na rundunar 'yan sandan Najeriya (EOD) ta ce ta gano wani bam da aka saka a harabar Hukumar zabe mai zaman kanta INEC na garin Owerri a jihar Imo.

The Punch ta ruwaito cewa rundunar ta ce an kai bam din samfurin 80mm zuwa hedkwatan na EOD a jihar inda ta ce an kuma gano wasu bama-baman uku a harabar kamfanin siminti na BUA da ke Okpella a jihar Edo a ranar 1 ga watan Oktoban 2019.

Rundunar ta ce, "A ranar 16 ga watan Augustan 2019, jami'a daga sashin EOD a Owerri sun gano gano 80mm bam a harabar INEC a Umuguma, karamar hukumar Owerri ta kudu a jihar Imo. An kai bam din zuwa wurin ajiye na rundunar da ke Owerri.

DUBA WANNAN: Hotunan gangariyan sabbin jiragen kasa na zamani da China ta kera wa Najeriya

"A kuma ranar 27 na Augustan 2019 misalin karfe 8.30 na dare, jami'an EOD tare da hadin gwiwan 'yan sanda na Abuja sun gano wasu kayayakin hada bam a tashan mota na El-Rufai a Nyanya Abuja. An kama mutum biyu da ake zargi da hannu cikin lamarin kuma ana cigaba da bincike."

Rundunar 'yan sandan ta bayyana hakan ne ranar Litinin a Legas yayin da ta ke karbar wasu na'urorin gano bama-bamai da sashin binciken nukilya na Amurka ya bawa Najeriya.

Kwamishinan 'yan sanda sashin EOD, Maikudi Shehu ya ce na'urorin za su taimakawa rundunar wurin gano bama-bamai da ake shigowa da su kasar da haramtattun hanyoyi.

Babban mai bayar da shawara na kasar Amurka, Bryceon Shulman ya ce wannan gudunmawar da suka bayar alama ce na yunkurin kulla alakar arziki da hadin gwiwa da Najeriya a yunkurin ta na yaki da safarar kayayyakin nukiliya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel