Da duminsa: An sake bankado gidajen ladabtar da fandararru 2 marasa rijista a jihar Kaduna

Da duminsa: An sake bankado gidajen ladabtar da fandararru 2 marasa rijista a jihar Kaduna

Bayan biyun da aka bankado a unguwar Rigasan jihar Kaduna, gwamnatin jihar Kaduna ta sake bankado gidajen ladabtar da kangararru biyu marasa rijista a jihar.

Wannan karon, a garin Zariya aka gano gidajen biyu.

Tuni an garzaya da wadanda aka samu cikin gidajen cikin mari zuwa gidan gwamnatin jihar.

Mataimakiyar gwamnan jihar, Hadiza Balarabe, ce ta karbi bakuncinsu tare da sauran manyan jami'an gwamnatin jihar Kaduna.

Hajiya Hadiza ta bayyana cewa za'a kai su asibiti domin dubasu kafin sanin matakin da za'a dauka na gaba.

Ana zargin wani gida na uku mai dauke da yara 40 amma har yanzu ba kammala bincike ba.

Kalli hotunan:

Da duminsa: An sake bankado gidajen ladabtar da fandararru 2 marasa rijista a jihar Kaduna
Zariya
Asali: Facebook

Da duminsa: An sake bankado gidajen ladabtar da fandararru 2 marasa rijista a jihar Kaduna
Hadiza da yaran
Asali: Facebook

KU KARANTA: An cigaba da harar 'yan Najeriya da ke kasar Afirka ta kudu

Da duminsa: An sake bankado gidajen ladabtar da fandararru 2 marasa rijista a jihar Kaduna
Da duminsa: An sake bankado gidajen ladabtar da fandararru 2 marasa rijista a jihar Kaduna
Asali: Twitter

A wani labarin mai kama da haka, Shugaban daya daga cikin shahararrun makarantun ladabtar da kangararru da ke jihar Kano, Sheikh Muhammadu Aminu Abubakar, yayin wata hirarsa da manema labarai na BBC Hausa ya fadi dalilin rufe cibiyarsa ta mari.

Sheikh Muhammadu Aminu Abubakar wanda ya kasance shugaban makarantar nan ta mari da ke unguwar Arzai, wadda ta fi shahara da Manzo Arzai, ya sallami dukkanin dalibansa tare da rufe makarantar da ke cikin birnin Kanon Dabo.

Lamarin na zuwa ne bayar irin dirar mikiya da rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi wa wasu makarantun mari da ke wasu sassa a Arewacin kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel