Bayan shekara 12: Kotubta tsayar da ranar yanke wa tsohon gwamnan PDP, Sanatan APC hukunci a kan zargin badakalar biliyoyi

Bayan shekara 12: Kotubta tsayar da ranar yanke wa tsohon gwamnan PDP, Sanatan APC hukunci a kan zargin badakalar biliyoyi

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar Legas ta tsayar da ranar 2 ga watan Disamba domin zartar da hukunci a kan zargin badakala da almundahana da kudin jama'a da hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki ke yi wa tsohon gwamnan jihar Abiya, Sanata Orji Uzor Kalu.

Alkalin kotun, Jastis Mohammed Idris, ya tsayar da ranar yanke hukuncin ne a ranar Talata bayan lauyoyin masu kara da wadanda ake kara sun kammala gabatar da hujjojinsu.

EFCC ta gurfanar da Kalu da Udeh Udeogu, darektan wani kamfani mai suna Slok, bisa tuhumarsu da laifuka 39 da suka hada da almundahanar kudin da yawansu ya kai biliyan N7.6.

An fara gurfanar da Kalu ne a shekarar 2007 bayan ya sauka daga kujerar gwamna, amma saboda tangardar da aka samu a shekarun baya, sai yanzu kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci.

DUBA WANNAN: Ganduje: Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunce a kan sabbin masarautun Kano

Bayan zargin karkatar da biliyan N7.6 da ake yi wa tsohon gwamnan, EFCC na tuhumarsa da laifin fitar da miliyan N460 daga asusun jihar Abia a tsakanin watan Yuli zuwa Disamba na shekarar 2002.

Tun da farko, Kalu ya nemi ya zuke ta hanyar bayyana cewa bashi da wani laifi, a saboda haka babu bukatar ya amsa wata tuhuma da EFCC ke masa.

Tsohon gwamnan ya shaida wa kotun cewa shi tsohon attajiri ne da ya dade da mallakar makudan kudi da kadarori, tare da bayyana cewa shine ya biya kudin da aka yi wa jam'iyyar PDP rijista, sannan ya bawa Obasanjo gudunmawa mafi tsoka a shekarar 1999 domin ya yi yakin neman zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel