Ajali ya yi kira: Ruwan kududdufi ya cinye wani mutumi dan shekara 40 a jahar Kano

Ajali ya yi kira: Ruwan kududdufi ya cinye wani mutumi dan shekara 40 a jahar Kano

Wani mutumi dan shekara 40 mai suna Mohammed Mohammed ya gamu da ajalinsa a cikin wani kududdufi dake cikin garin Kano yayin da ya tunjuma kududdufin da nufin yin wanka, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a wani kududdufi dake kwanatr tattarawa cikin karamar hukumar Dawakin Tofa na jahar Kano, kamar yadda kaakakin hukumar kwana kwana ya bayyana.

KU KARANTA: Idan da ranka ka sha kallo: Mamaci ya nemi a budeshi daga kabarinsa ya dawo duniya

Kaakakin hukumar, Malam Saidu Mohammed ya bayyana haka a ranar Talata, 22 ga watan Oktoba inda yace lamarin ya auku ne da sanyin safiyar Talata inda mamacin ya shiga cikin kududdufin don yin wanka.

“Da misalin karfe 10.05 na safiyar Talata muka samu kira daga wani mutumi mai suna Malam Rabiu Abbas wanda ya shaida mana cewa ya hangi gawar Mohammed tana yawo a saman ruwan kududdufin.

“Samun wannan bayani keda wuya muka garzaya da tawagarmu zuwa kududdufin da misalin karfe 10:25 na safe, sa’annan muka garzaya da Mohammed zuwa asibitin kwararru na tunawa da Murtala dake Kano, inda a can likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.” Inji shi.

A wani labari kuma, wani lamari mai kama da almara ya faru a kasar Ireland wanda ya daure ma mutane da dama kai, suka gaza fahimtarsa har sai daga baya, wannan lamari kuwa shine yadda wani mamaci ya yi magana bayan an turbudeshi a cikin kabarinsa.

Wani mutumi mai suna Shay Bradley ya rasu, inda yan uwa da abokan arziki suka garzaya zuwa makabarta domin a binneshi a gabansu, sai dai jim kadan bayan rufeshi sai suka ji shi yana magana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel