Yaki da rashawa: EFCC ta kama wani babban yaro Ismaila Mustapha

Yaki da rashawa: EFCC ta kama wani babban yaro Ismaila Mustapha

Jami’an hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC sun kama wani fitaccen babban yaro daya shahara a shafin sadarwar zamani ta Instagram mai suna Ismaila Mustapha ‘Mompha’.

Rahoton jaridar Daily Trust ta ruwaito kaakakin hukumar EFCC,Wilson Uwujaren ne ya bayyana haka a ranar Talata, 22 ga watan Oktoba, inda yace Yansanda sun kama wannan matashi ne a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Kotu ta sadaukarwa gwamnati gidaje, gonaki da filayen AbdulRashid Maina 23, kalli jerinsu

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin na EFCC, Wilson bai kara wani fitar da wani bayani game da wannan lamari ba, amma dai ya tabbatar da cewa har zuwa lokacin tattara wannan rahoto Mompha na hannun hukumar.

Shi dai Mompha, mutane da daman a masa kirari da sarkin yan canjin kudaden kasashen waje a Najeriya saboda tsananin kudinsa da kuma yadda yake baje kolin arzikinsa a shafukan sadarwar zamani da nufin neman suna da yin gabata.

Akwai wasu rahotanni dake nuna cewa Mompha ya tsere daga gidansa dake kasar Dubai don gudun kada jami’an hukumar Yansanda ta duniya, INTERPOL su kamashi, hakan tasa ya dawo Najeriya da zama.

A wani labari kuma, Babban kotun tarayya dake Abuja ta bada umurnin sadaukarwa gwamnatin tarayya dukiyoyi 23 da ake kyautata zaton na tsohon shugaban gyara harkan fansho, Abdulrashid Maina.

Alkali Folashade Ogunbanjo, ta bayyana umurnin ne ranar Talata yayinda take yanke hukunci kan karar da hukumar hana almundana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel