Kwamitin majalisar wakilai kan wutar lantarki na cikin ganawar sirri tare da Discos

Kwamitin majalisar wakilai kan wutar lantarki na cikin ganawar sirri tare da Discos

Kwamitin majalisar wakilai kan lantarki a ranar Talata, 22 ga watan Oktoba, ya yi ganawar sirri da kamfanonin rabe-raben wutan lantarki wato Discos.

Shugaban kwamitin, Aliyu Magaji bayan hallaran manyan jami'an kamfanonin, ya bukaci yan jarida da hadimai dasu fita su bar dakin taron.

Kwamitin a makon da ya gabata ta gano wani rikitaccen lamari kan tsarin kasafin kudin da ma’aikatar Lantarki ta gabatar na 2020.

A wani lamarin kuma, mun ji cewa a kokarin da gwamnatin tarayya ta ke yi na ganin matsalar wutar lantarki ya zama tarihi a Najeriya, mun samu labari cewa Najeriya ta yi nasarar samun wasu bashin kudi da ta ke nema.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar The Cable, babban bankin Duniya ya amince da rokon da Najeriya ta gabatar na samun aron Dala biliyan 3 domin gyara wutar lantarki.

KU KARANTA KUMA: Kalli hotunan liyafar da uwargidar Yahaya Bello ta shirya bayan mijin aminiyarta ya zama mataimakin gwamnan Kogi

Babban bankin ya yi na’am da kokon barar gwamnatin tarayyar inda aka amince da ya ba ta wannan kudi da nufin fadada hanyoyin raba wutar lantarki inji babbar Ministar kudin kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel