'Bacewar Dadiyata alama ce ta babu adalci a Najeriya - CSO

'Bacewar Dadiyata alama ce ta babu adalci a Najeriya - CSO

Hadin gwiwar wasu kungiyoyi masu kare hakkin fararen hula bisa jagorancin kungiyar tabbatar da ci gaban dimokuridayya UDDF reshen jihar Kano, ta kirayi hukumomin tsaro, gwamnatin tarayya da kuma ta jihar Kaduna akan kara kaimi wajen lalubo matashin nan, Abubaka Idris mai inkiyar Dadiyata wanda ya bace tun a watan Agustan da ya gabata.

A waiwayen da jaridar Kano Focus ta yi, Dadiyata wanda ya kasance lakcara kuma jigo mai tashe a matasan shafin sada zumunta na Twitter wajen fafutikar kare siyasar Kwankwasiyya, ya yi batan dabo tun yayin da wasu mutane da a babu masaniyar ko su waye suke dauke shi daga gidansa da ke unguwar Barnawan birnin Kaduna a ranar Juma'a 1 ga watan Agusta.

Babu shakka Dadiyata ya shahara a kan bin akidar Kwankwasiyya wanda kuma ke biyayya sau-da-kafa ga tsohon gwamnan jihar Kano, kuma tsohon dan Majalisar Dattawa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

Ba ya ga haka ya kasance aboki ga dan takarar gwamnan jihar Kano na jam'iyyar PDP a zaben 2019, Abba Kabir Yusuf, kuma daya daga cikin matasan da suka yi fice wajen sukar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da na jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i.

A yayin ganawa da manema labarai cikin birnin Kanon Dabo, jagoran kungiyar UDDF, Isma'il Auwal, ya ce ranar Talata, 22 ga watan OKtoban 2019 ne Dadiyata ya cika kwanaki 83 da yin batan dabo, wanda ya zuwa yanzu babu amo ballantana labarinsa.

KARANTA KUMA: Hukumar NAFDAC ta koka da rashin ingancin Burodi a Najeriya

Mista Auwal ya hikaito irin halin kunci gami da damuwa da 'yan uwa da kuma iyalan Dadiyata suke ci gaba da fuskanta a halin yanzu, sanadiyar rashin tabbacin yana nan da rai ko kuma akasin haka.

Kiraye-kirayen a sako matashin wanda aka fi sani a kafafe na sada zumunta da suna Dadiyata, sun biyo bayan zargin da wasu jama'a ke yi na cewa jami'an tsaron farin kaya wato DSS ne suka kama shi, saboda yadda yake sukar manufofin gwamnatin tarayya, ta jihar Kano da kuma ta Kaduna.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel