Haramta Boko: 'Yan ta'adda sun kona makarantu a kasar Nijar

Haramta Boko: 'Yan ta'adda sun kona makarantu a kasar Nijar

Al'ummar jihar Tillabery dake jamhuriyyar kasar Nijar sun tsinci kansu cikin tsakanin taraddadi a yayin da wasu 'yan bindiga suka kone wasu makaranta, lamarin da ya haddasa rufe makarantu da dama a yankin da ke karkashin dokar ta-baci.

Kamar yadda mazauna yankin suka bayar da shaida, 'yan ta'addan rike da bindigu kuma haye a kan babura sun cinna wuta a wasu makarantun jihar Tillabery ba tare da cewa kowa uffan ba.

A rahoton da jaridar BBC Hausa ta wallafa, 'yan bindigar sun kone makarantun boko ne a yankin Makulandi da ke jihar Tillabery, lamarin da haskaka irin tabarbarewar harkokin tsaro a yankin.

Makamancin wannan ta'addancin ya auku a makon da ya gabata, inda wasu bata-gari suka kone makarantun boko da ke garuruwan Kiki da Bomoanga, wadanda ke nisan mita dubu 20 daga Arewa maso Yammacin garin Makulandi.

Wani mazauni a yankin na Makulandi da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa manema labarai halin kunci da al'ummar yankin suka tsinci kansu bayan kone makarantun.

A cewarsa, "ana cikin halin dar-dar saboda magana ta gaskiya malamai da daliban makarantun da aka kona duk sun watse kowa ya yi ta kansa," in ji shi.

Kazalika ya ce a yayin da dama daga cikin malaman makarantun basu kasance mazauna garin ba, lamarin da ya sanya suka koma garuruwansu haka kuma dalibai ke zaman kashe wando a gidajensu.

KARANTA KUMA: EFCC ta gurfanar da 'yan kasar Birtaniya biyu da laifin zamba

Wannan na zuwa ne kwana biyu bayan 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka yi awon gaba da magajin garin Kabalewa a yankin Diffa mai iyaka da jihar Borno a Najeriya.

Lamarin na zuwa na ne kwanaki biyu bayan da 'yan bindiga wadanda ake zargi 'yan Boko Haram ne suka yi awon gaba da magajin garin Kabalewa da ke yankin Diffa mai iyaka da jihar Bornon Najeriya.

A tsawon shekaru goman da shude, har yanzu kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram na ci gaba da kasancewa barazana ga kasashen da ke iyaka da tafkin Chadi.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel