EFCC ta gurfanar da 'yan kasar Birtaniya biyu da laifin zamba

EFCC ta gurfanar da 'yan kasar Birtaniya biyu da laifin zamba

Hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arziki zagon kasa a Najeriya, ta bayyana tuhumar wasu baki 2 'yan kasar Birtaniya da ta ke zarginsu da aikata laifuka 16 na fidda kudade ta hanyar da ta sabawa dokar kasar nan.

Kamar yadda hukumar ta bayyana a shafinta na zauren sada zumunta, ta ce mutanen biyu da ta ke zargi; James Richard Nolan da kuma Adam Quinn, daraktoci ne a kamfanin nan na P&ID dake tsibirin Ireland.

A baya-bayan nan ne dai kamfanin ya samu nasara a gaban watan kotun kasar Birtaniya, yayin da ta umarci gwamnatin Najeriya ta sarayar masa da kadarorinta na kimanin dalar Amurka Biliyan 9.6, biyo bayan karar da ya shigar a kan sabawa sharudan wata yarjejeniya makamashin iskar gas da ya kulla da kasar nan.

Sai dai ya zuwa yanzu, lauyan Mista Quinn da Nolan ya musanta zargin da hukumar EFCC ta ke yi wa wadanda ya ke wakilta.

A halin yanzu hukumar EFCC na neman Mista Quinn ruwa a jallo, yayin da tuni ta sakaya Mista Nola a katararta gabanin ya cika sharudan beli.

KARANTA KUMA: Hukumar 'yan sandan Najeriya ta yi wa manyan jami'ai 507 karin girma

Sanarwar da hukumar EFCC ta wallafa a shafinta na Facebook, ta yi ikirarin cewa kamfanin P&ID (Process & Industrial Developments Ltd), ya yi wa dala 125,000 wata basaja ta yaudara da ke cikin asusun ajiyasar a kasar.

Haka kuma EFCC ta ce kamfanin P&ID ya hau kujerar naki ta fayyace wa ma'aikatar kula da harkokin kasuwancin Najeriya dukkanin harkokin da ya ke gudanarwa a kasar nan.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel