An daure Basudane tsawon shekaru biyu da laifin fataucin muggan kwayoyi a Najeriya

An daure Basudane tsawon shekaru biyu da laifin fataucin muggan kwayoyi a Najeriya

Wata babbar kotun tarayya da ke jihar Legas, yayin zamanta na ranar Litinin da ta gabata ta zartar da hukuncin dauri na tsawon shekaru biyu kan wasni matashi dan asalin kasar Sudan da laifin fataucin miyagun kwayoyi.

Kotun yayin zamanta bisa jagorancin Justice Salihu Sa'idu Abdallah, ta zartar da hukuncin ne akan Guma Isma'il Mahdi Abdallah, bayan kama shi da laifin shigo da kilo 1.44 na wata kwaya mai sanya matsanancin maye mai sunan Methamphetamine.

Gabanin zartar da hukuncin, Abdallah wanda bai samu lauyan da zai kare shi ba a gaban kotu, ya nemi da ta yi masa rangwami tare da sassauta hukuncin da zartar a kansa.

Ya shaidawa Alkalin kotun cewa, wannan shi ne karo na farko da ya aikata laifin kuma baya ga haka ba ya da wani dangi ko guda a Najeriya illa iyaka tsautsayi da ya hankado shi kasar.

Lauyan hukumar NDLEA mai yaki da masu ta'ammali da miyagun kwayoyi, Ali Ibrahim, ya tabbatar wa da kotun cewa, babu shakka wannan shi ne karo na farko da aka kama Basudanen da laifi.

A yayin zartar da hukuncinsa, Justice Sa'idu ya umarci hukumar NDLEA ta hallakar da muguwar kwayar da aka kama a hannun matashin kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

KARANTA KUMA: Kwankwaso ya kaddamar da makarantar koyon aikin jinya da ungozoma ta jihar Kano a ranar murnar bikin zagayowar ranar haihuwars

Zayyanar shaidu a gaban kotun ta tabbatar da cewa, an cafke Abdalla ne dai da muguwar kwayar tun a ranar 24 ga watan Yunin 2019, a filin sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa na Murtala Muhammad ana tsaka da tantance fasinjojin jirgin Ethiopia Airline da za su yi balaguro zuwa birnin Addis Ababan kasar Habasha.

Haka kuma kotun ta saurari shaidar cewa, laifin da Basudanen ya aikata ya sabawa dokokin hukumar NDLEA wadda aka shimfida tun a shekarar 2004.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel