CBN da sauran bankunan Najeriya sun juya wa MTN baya bayan Pantami ya tsoma baki

CBN da sauran bankunan Najeriya sun juya wa MTN baya bayan Pantami ya tsoma baki

Gwamnatin Najeriya da babban bankin kasa (CBN) sun yi watsi da yunkurin kamfanin sadarwa nnna MTN a kan cire wa kwastomominsu N4 (Naira hudu) duk lokacin da suka saka katin waya ta hanyar amfani da tsarin USSD.

A ranar Litinin ne kamfaninn sadarwa na MTN ya sanar da cewa zai fara cire N4 a duk dakika 20 da kwastoma ya shafe yayin amfani da tsarin USSD. Kamfanin sadarwaar ya ce zai yi hakan ne bisa bukata da kuma amincewar dukkan bankunan da ke Najeriya.

Sai dai, kungiyar shugabannin dukkan bankunan da ke Najeriya sun bayyana cewa basu da wata masaniya a kan ikirarin MTN a kan cewa sune suka bukaci hakan.

A cikin jawabin da suka fitar ranar Litinin, shugabannin bankunan sun bayyana cewa, "bankuna basu bukaci MTN ta fara cire kudin kwastomomi ba kamar yadda suka bayyana a cikin sakonnin da suka aika wa jama'a ba.

"Babu hannun bankuna a cikin shawarar da MTN ta yanke na fara cin tarar kwastomomi a kan tsarin USSD, su ne ke cire kudin kwastominsu idan sun aika sako ko sun kira waya ko kuma idan sun yi amfani da yanar gizo ba bankuna ba, a saboda haka sune suka yanke wannan shawara ba bankuna ba."

DUBA WANNAN: Kano: 'Yan daba sun kai wa tawagar Kwankwaso hari, sun raunata jama'a, sun lalata motoci

Jama'a sun wayi gari da samun sako a wayoyinsu na hannu a kan wannan sabon tsari da kamfanin sadarwa na MTN ke shirin fara aiki da shi daga ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba, 2019.

Ofishin minstan sadarwa, Dakta Isa Ali Pantami, ya ankarar da ma'aikatar sadarwa a kan wannan sabon tsari da MTN ke shirin kaddamar wa bayan jama'a sun mika kukansu gare shi a dandalin sada zumunta na Tuwita a ranar Lahadi.

Pantami ya ce bashi da masaniya a kan sabon tsarin da kamfanin sadarwa na MTN ya bullo da shi, a saboda haka ne ya umarci hukumar kula da kamfanonin sadarwa da ke Najeriya (NCC) da ta tabbatar da cewa MTN ta dakatar da wannan sabon tsari da ta bullo da shi kuma take shirin kaddamar wa.

Da yake jinjina wa Pantami a kan daukan mataki a kan lokaci, Joe Abba, tsohon hadimi a gwamnatin Buhari, ya ce yanzu haka kamfanin sadarwa na MTN ya dakatar da sabon tsarin sakamakon umarnin da Pantami ya bayar.

Jama'a na yawan korafi a kan yadda kamfanonin sadar wa a Najeriya ke bullo da tsare-tsare masu suna daban-daban domin raba su da 'yan sulallansu na yin kira a waya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel