Gwamnati ta rabar da dala miliyan 103.64 wanda Abacha ya sata ga talakawa

Gwamnati ta rabar da dala miliyan 103.64 wanda Abacha ya sata ga talakawa

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta rabar da makudan kudade dala miliyan 103.64 wadanda tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin Soja, Janar Sani Abacha ya sata daga baitil malin kasar nan, ga talakawan Najeriya.

Jaridar Punch ta ruwaito hadima ta musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan sha’anin bayar da tallafi, Maryam Uwais ce ta bayyana haka a ranar litinin, 21 ga watan Oktoba, inda tace gwamnati na zuba kudaden Abachan a cikin tallafin da take baiwa yan Najeriya.

KU KARANTA: Yaki da Boko Haram: Buhari zai sayo sabbin jiragen yaki daga kasar Rasha

A jawabinta, Uwais tace zuwa yanzu gwamnati ta kashe $76,538,530 daga kudaden Abacha da kuma $27,099,028 daga bashin da International Development Association take baiwa Najeriya, duk a harkar tallafa ma yan Najeriya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Uwais na cewa da kudaden ake amfani wajen biyan masu cin gajiyar tsarin bayar da N5000 ga marasa karfi, wanda tace hakan ya sauya rayuwan mutane da dama.

Ta kara da cewa gwamnatin Najeriya tare da bankin duniya da kuma gwamnatin kasar Swiss ne suka taru suka yanke hukuncin yadda ya kamata a kashe wadannan kudade da Janar Abacha ya yi sama da fadi dasu.

“A watan Disambar 2014 wata kotun Swiss ta yanke hukunci a kan haramcin $322.5m da Abacha ya sata, sa’annan ta bayar da umarnin a mayar dasu Najeriya da sharadin sai bankin duniya ta sanya idanu a kan yadda za’a kashe wadannan makudan kudade.” Inji ta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel