Yanzu - Yanzu: An cigaba da harar 'yan Najeriya da ke kasar Afirka ta kudu

Yanzu - Yanzu: An cigaba da harar 'yan Najeriya da ke kasar Afirka ta kudu

- A yau ne aka gano sabon harin da 'yan kasar Afirka ta kudu suka cigaba da kaiwa 'yan Najeriya mazauna can kasar

- Kamar yadda wata majiya ta bayyana kuma jaridar The Nation ta ruwaito, an hari 'yan Najeriyar ne a Mpumalanga

- Tuni da shuwagabannin 'yan Najeriya mazauna kasar da babban wakilin Najeriya a kasar suka bazama don tattara bayanai

An gano cewa, an samu sabon hari a kasar Afirka ta kudu akan 'yan Najeriya.

Kamar yadda majiya mai karfi ta sanar, an hari 'yan Najeriyar ne a Mpumalanga.

A halin yanzu, shuwagabannin 'yan Najeriya a kasar Afirka ta Kudu da kuma babban wakilin Najeriya a kasar Afirka ta kudun na tattara bayanai akan hakan.

KU KARANTA: An karrama Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano

Idan ba zamu manta ba, a kwanakin baya ne aka dinga kaiwa bakin haure hari a kasar Afirka ta kudun. Hakan kuwa ya jawo tashin hankula a wajen 'yan Najeriya da ma sauran mutanen da ba 'yan kasar ba amma mazauna kasar.

'Yan Najeriya mazauna kasar sun tafka asara da yawa akan hakan.

Tuni gwamnatin Najeriya ta tashi tsaye don ganin ta dawo da 'yan kasar gida don karae rayukansu.

Hakan kuwa aka yi, don shugaban kamfanin jiragen sama na Air Peace ne ya dau nauyin jigilar 'yan Najeriya zuwa gida.

A don haka kuwa, har majalisar dattawan kasar nan ta jinjinawa mai kamfanin akan aikin nuna kishin kasa da ya aiwatar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel